logo

HAUSA

Kasar Sin na goyon bayan duk wani kokarin warware rikicin Ukraine cikin lumana

2024-06-03 20:09:44 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin a yau Litinin ta jaddada cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, ya kamata a goyi bayan duk wani kokari da zai taimaka wajen warware rikicin Ukraine cikin lumana.

Da take amsa wata tambaya kan taron zaman lafiya na Ukraine da za a yi kasar Switzerland, Mao Ning ta ce, a ko da yaushe kasar Sin tana mai da hankali kan cewa, taron zaman lafiya na kasa da kasa na bukatar cimma muhimman abubuwa guda uku na amincewa daga kasashen Rasha da Ukraine, da halartar dukkan bangarori cikin adalci, da kuma yin tattaunawa kan dukkan shirye-shiryen zaman lafiya cikin adalci, in ba haka ba, da wuya taron na zaman lafiyar zai taka muhimmiyar rawa wajen maido da zaman lafiya. Mao ta kara da cewa, ajandar taron bai cimma abubuwan guda uku ba, wanda hakan ya sa kasar Sin ke kafa-kafa wajen halartar taron. Ta yi nuni da cewa, matsayin kasar Sin game da taron a bayyane yake, ba tare da nuna son kai ba, ba wai tana tare da wani bangare ba, kuma ko shakka babu ba ta adawa da taron.

Mao ta ce, bai kamata a ce wasu kasashe ko tarurruka na musamman su ne ke yanke hukunci kan wanda ke goyon bayan zaman lafiya ko a'a ba, ta kara da cewa, ko da kasashe daban daban sun shiga taron, watakila ba za su yi fatan ganin an tsagaita bude wuta ba. (Yahaya)