logo

HAUSA

Sin ta kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa bisa ayyukanta masu amfani

2024-06-03 11:18:21 CMG Hausa

An rufe taron tattaunawar Shangri-La karo na 21 a Singapore jiya Lahadi. Bayan rufe taron, masanan tawagar Sin dake halartar taron sun zanta da ’yan jarida na Sin da na kasashen waje. 

Masanan sun bayyana cewa, Sin ta kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa bisa ayyukanta masu amfani, ta yadda ta ba da gudummawa wajen samar da kayayyakin kiyaye tsaron jama’a ga zamantakewar kasa da kasa.

Masanan sun kara da cewa, bangaren Sin zai ci gaba da samar da kayayyakin kiyaye tsaron jama’a ga kasa da kasa, wanda ya hada da aiwatar da ajandar tsaron kasa da kasa, da inganta sulhu tsakanin Saudiya da Iran, da kuma inganta warware rikicin Ukraine, da rikicin Falasdinu da Isra’ila cikin lumana. 

Kaza lika, a nan gaba bangaren Sin zai ci gaba da gudanar da hadin gwiwa tare da bangarorin da abin ya shafa na kasashen yankin Asiya-Pasifik, da ma sauran sassan duniya, don gina al’umma mai makoma bai daya ga daukacin yankunan Asiya-Pasifik tare. (Safiyah Ma)