Xi ya aike da wasikar taya murnar cika shekaru 30 da kafa CAE
2024-06-03 20:55:02 CMG Hausa
A yau Litinin ne Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga kwalejin nazarin injiniyancin kasar Sin (CAE) da ya taka rawar gani a fannin kimiyya da fasaha bisa manyan tsare-tsare, tare da ba da sabbin gudummawa wajen ganin kasar Sin ta dogaro da kanta da kuma zama kasa mai karfi a fannin kimiyya da fasaha.
Xi ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar taya murna da ya aikewa kwalejin na CAE dangane da cika shekaru 30 da kafuwarsa. An kafa CAE ne a shekarar 1994, wanda shi ne babbar cibiyar ilimi da ba da shawara a kan kimiyyar injiniyanci da fasaha ta kasar Sin. (Yahaya)