Wakilin Sin: Kasar Sin ta goyi bayan Falasdinu wajen taka rawar gani a WHO
2024-06-02 17:22:03 CMG Hausa
Zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, Chen Xu, ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan Falasdinu wajen taka rawar gani a Hukumar lafiya ta duniya (WHO).
Chen ya bayyana hakan ne a jawabinsa na ranar Juma'a a yayin babban taron kiwon lafiya na duniya karo na 77 (WHA).
WHA ta amince da wani daftarin kuduri kan "daidaita shigar Falasdinu cikin hukumar ta WHO tare da shiga MDD", bayan kuri'ar amincewa 101, 5 na nuna adawa, 21 kuma suka kaurace.
Chen ya ce, babban taron gaggawa na MDD ya amince da wani kuduri a kwanan nan da gagarumin rinjaye, inda ya amince da cancantar Falasdinu ta zama mamba a MDD. Chen ya bayyana cewa, Sin na maraba da kudurin, saboda ya yi daidai da muradin kasashen duniya.
Chen ya jaddada cewa, kasar Sin tana kallon tsarin samar da kasashe biyu a matsayin hanya daya tilo da ta dace don warware rikicin Falasdinu da Isra'ila, tare da baiwa Falasdinu damar zama cikakken mamban MDD a matsayin muhimmin mataki na cimma wannan buri. (Yahaya)