logo

HAUSA

Ministocin sufuri da kasuwanci na kasar Togo sun gana da shugaban kasar Nijar

2024-06-02 16:11:43 CMG Hausa

Shugaban kwamitin ceton kasa CNSP kuma shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tiani ya gana a ranar 31 ga watan Mayu tare da ministocin kasar Togo guda biyu a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai, inda bangarorin biyu suka mai hankali kan muhimman abubuwan moriyar kasashen biyu.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu ya aiko mana da wannan rahoto.

 

Su dai wadannan ministocin kasar Togo sun hada da ministan sufurin kasa da sararin samaniya da kuma jiragen kasa, mista Affoh Atcha Dedji da kuma ministar kasuwanci da ayyukan hannu da kuma bukatun jama’a madam Kayi Mivedor-Sambiani. Wannan ganawa tare da shugaban kasar Nijar ta gudana a gaban idon takwararorinsu na kasar Nijar, Seydou Asman ministan kasuwanci, da ministar ayyukan hannu madam Soufiane Aghaichata Guichene da kuma manjo kanal Salissou Mahaman Salissou ministan sufuri.

Mista Affoh Atcha Dedji ya bayyana wa manema labarai cewa sun je fadar shugaban kasar Nijar domin isar wa shugaban kasa Abdourahamane Tiani da rahoton aikinsu da kuma isar da sakon dan uwansa kuma amininsa, shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe.

Inda ya kara da cewa, tun yau da watanni goma, dangantaka tsakanin Nijar da Togo ta kara karfafa, bayan ziyarar shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tiani a birnin Lome na kasar Togo. An bada umurni domin kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu. An dauki wani adadin matakai masu nagarta, musamman ma domin karfafa karfin tashar ruwa Lome, ta yadda kayayyakin Nijar za su iyar shigowa da wucewa yadda ya kamata, in ji ministan Togo.

Dole mu saukaka jigilar kayayyakin Nijar kan hanyar Lome-Ouagadougou-Niamey. Mun samu gudanar da wasu ayyuka a yayin wannan ziyara, domin ganin cikin wane yanayi za mu iyar kara karfafa da saukaka ayyuka tare tashar ruwan Lome, tare da ‘yan kasuwar Nijar, a cewar minista Affoh Atcha Dedji.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.