logo

HAUSA

Taron karawa juna sani kan wayewar kan kasar Sin ta zamani ya bukaci karin nasarori a fannin ilimi

2024-06-02 21:37:06 CMG Hausa

An kaddamar da wani taron karawa juna sani kan raya wayewar kan zamani ta kasar Sin a yau Lahadi a nan birnin Beijing.

Li Shulei, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban sashen yada labarai na kwamitin kolin JKS, ya gabatar da muhimmin jawabi a yayin taron, wanda kwalejin nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin ya shirya. 

Mahalarta taron sun jaddada bukatar samun karin nasarori a fannin ilimi da suka hada ilimin tsohon zamani da na sabon zamani, da kuma al'adun kasar Sin da na yammacin duniya, domin samar da ci gaban ilimi da al'adu.

Bugu da kari, sun amince cewa, ya zama wajibi a ci gaba da dunkule muhimman ka'idoji na tsarin Markisanci da takamaiman yanayi na musamman da kyawawan al'adun gargajiya na kasar Sin, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar tsarin kirkire-kirkire na jam'iyyar. (Yahaya)