logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta bullo da wata sabuwar manufa da za ta habaka sha’anin zuba jari a bangaren samar da madara

2024-06-02 16:12:53 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana shirin samar da wata sabuwar manufa da za ta kyautata sha’anin zuba jari a bangaren samar da madarar shanu da zummar kawo karshen yawan shigo da madara daga kasashen ketare.

Karamin minista a ma’aikatar bunkasa ayyukan gona da samar da abinci na kasar Sanata Aliyu Sahabi Abdullahi ne ya tabbatar da hakan jiya Asabar 1 ga wata a birnin Abuja yayin bikin ranar madara ta duniya na shekara ta 2024.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Ministan ya ce yanzu haka Najeriya ita ce kasar da ta fi yawan shigo da madara daga waje, duk kuwa da cewa kasar tana da yawan shanun da aka kiyasta sun kai miliyan 60.

Ya kara da cewa, a bayanan da babban bankin Najeriya ya fitar, ya nuna cewa gwamnati tana kashe dala biliyan 1.5 a duk shekara wajen shigo da madara daga waje.

Ko da yake dai kamar yadda bincike ya nuna, akasarin shanun da Fulanin Najeriya ke da su ba sa iya samar da madarar da za ta iya biyan bukatun ‘yan kasar.

To amma karamin ministan ma’aikatar gonar ta tarayyar Najeriya ya ce sabuwar manufar da gwamnati za ta fito da ita, za ta karfafa tsarin baye ta hanyar kimiyyar zamani wanda zai karawa shanun mu na gida sinadaran da za su ba su damar samar da madara mai yawa, haka kuma manufar za ta taimaka wajen maganin matsalolin da ake fuskanta wajen kiwon dabbobi.

“Za mu kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a karkashin shirin sabunta fata ga kasa, inda za mu bayyana mahimmancin madara wajen gina jiki da lafiya musamman ma ga yara da kuma mata masu juna biyu, muna da kyakkyawan fatan cewa, aiwatar da wannan manufa zai dora Najeriya bisa tafarkin cinikin madara sannan kuma zai tabbatar da wadatuwar madara a kasa tare da bunkasa yanayin rayuwar al’umma gaba daya.”(Garba Abdullahi Bagwai)