logo

HAUSA

An gabatar da sakamakon babban zaben Afirka ta Kudu a mataki na farko

2024-06-02 16:42:49 CMG Hausa

Bisa sakamako na mataki na farko da kwamitin zaben kasar Afirka ta Kudu mai zaman kansa ya bayar jiya Asabar ranar 1 ga wannan wata, an ce, jam’iyyar ANC ta samu kuri’u kashi 40.25 cikin dari a zaben majalisar dokokin jama’ar kasar, wadda ta kasance matsayin farko.

Manazarta sun bayyana cewa, jam’iyyar ta ANC ba ta samu kuri’u fiye da kashi 50 cikin dari ba, don haka ba ta samu rinjaye a zaben ba, sai dai jam’iyyar za ta nemi hadin kan sauran jam’iyyun kasar don tabbatar da ci gaba da kasancewar jam’iyyar dake kan mulkin kasar.

Bisa kundin tsarin mulkin kasar Afirka ta Kudu, bayan da aka zabi sabbin membobin majalisar dokokin jama’ar kasar, membobin majalisar za su gudanar da taro don zabar sabon shugaban kasar. (Zainab Zhang)