Ministan tsaro: Kasar Sin na adawa da kulla kebabben kawancen soji
2024-06-02 20:56:51 CMG Hausa
Ministan tsaron kasar Sin Dong Jun ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta yi kira da a hada kai don samar da zaman lafiya, kana tana adawa da kulla kebabben kawancen soja dauke da mummunar manufa.
Dong, a cikin jawabin da ya gabatar a taron tattaunawa na Shangri-La karo na 21 da aka gudanar a kasar Singapore, ya ce, “kananan kawance” daban daban dake harin wasu kasashe ba za su iya tabbatar da zaman lafiya a yankin ba, sai dai su haifar da karin tashin hankali.
Ya ce, sojojin kasar Sin za su dauki karin matakai a bayyane, da yin aiki tare da sojojin dake kasashen yankin, wajen gina wani sabon nau'in hadin gwiwar tsaro dake nuna daidaito, da amincewa da juna, da hadin gwiwar samun nasara tare.
Dong Jun ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na kara azama kan yin shawarwarin zaman lafiya bisa kyakkyawan nufi kan rikicin Ukraine, kuma ba ta taba bayar da makamai ga kowane bangare na rikicin Ukraine ba. (Yahaya)