logo

HAUSA

Tsarin kiwon lafiyar yaran kasar Sin na kara kyautata, in ji jami’in hukumar lafiyar kasar

2024-06-01 17:19:02 CMG Hausa

Jami’ar hukumar lafiya ta kasar Sin Shen Haiping, ta ce a shekarar 2023 da ta gabata, adadin yara kanana dake rasuwa a kasar ya yi matukar raguwa, inda adadin jarirai dake rasuwa ya yi kasa zuwa kimamin 4.5 cikin duk jarirai 1000, yayin da yara kanana da shekarun su ba su wuce 5 ba, adadin rasuwar su ya ragu zuwa kimamin 6.2 cikin duk 1000, adadin da ya nuna raguwar rasuwar rukunonin yaran biyu da kaso 56.3 bisa dari, da kuma kaso 53 bisa dari, idan an kwatanta da na shekarara 2012. Shen ta ce wannan adadi shi ne mafi kyawu da kasar ta cimma a tarihi.

Jami’ar wanda ta yi tsokacin a jiya Juma’a yayin taron manema labarai, ta ce "Daukacin manyan mizanin awon ingancin lafiyar yara kanana na kasar Sin sun ci gaba da inganta, inda suka tsallake na kasashe masu al’ummu dake samun matsakaici, da kololuwar kudaden shiga.”

Alkaluman kididdiga da aka gabatarwa manema labarai sun nuna cewa, a yanzu haka, akwai asibitocin yara 158, da na lura da mata masu juna biyu da lafiyar yara kanana 3,082 a sassan kasar Sin. Kaza lika, adadin gadajen kwantar da yara a asibitoci ya kai kimanin 2.7 kan duk yara 1000, adadin da ya karu daga 0.27 a shekarar 2015.

Shen ta kara da shan alwashin cewa, za a kara kwazo wajen kyautata ikon tsarin kiwon lafiyar kasar Sin, ta fuskar kula da majinyata da bayar da hidimomin lafiya ga yara. (Saminu Alhassan)