A ko da yaushe kasar Sin tana mai da hankali sosai kan damuwar Zambiya game da batun basussuka
2024-05-31 19:52:11 CMG Hausa
Yayin da take amsa tambayoyi game da sake fasalin tsarin basussukan kasar Zambiya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, a matsayinta na aminiya ga kasar Zambiya, kasar Sin a ko da yaushe tana mai da hankali sosai kan damuwar Zambiya don gane da batun basussuka, kuma ita ce kasa ta farko da ta tsawaita wa Zambiya wa’adin biyan basussuka.
An yi wa Mao Ning tambayar ce lokacin da take jagorantar taron manema labarai da aka saba gudanarwa na yau Jumma’a, 31 ga watan Mayu.
Jami’ar ta kara da cewa, kasar Sin ta jagoranci gagarumin ci gaba a aikin sake fasalin tsarin basussuka na kasar Zambiya, kuma ta samu amincewa sosai daga bangaren Zambiya da sauran kasashen duniya.
Kaza lika, ta bayyana cewa, a yayin da ake tinkarar batutuwan bashi da suka shafi kasashe masu tasowa, kasar Sin tana daukar matakai na dogon lokaci wajen taimakawa ci gaban kasashen da abin ya shafa. Har ila yau, Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su yi aiki tare da ita don ci gaba da tallafawa kasashen Afirka ciki har da kasar Zambiya, wajen samun ingantaccen ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta hanyar ayyuka masu inganci. (Bilkisu Xin)