logo

HAUSA

An shirya babban taron tinkarar sauyin yanayi tsakanin mabambantan wuraren Sin da Amurka

2024-05-31 15:20:26 CMG Hausa

 

An shirya babban taron tinkarar sauyin yanayi tsakanin wurare daban-daban na Sin da Amurka a jiya Alhamis, a Berkeley na jihar California, bisa sanarwar da bangarorin biyu suka bayar dangane da inganta hadin kansu a fannin tunkarar matsalar sauyin yanayi.

Manzon musamman na kasar Sin dake kula da aikin tinkarar sauyin yanayi Liu Zhenming, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo cewa, sauyin yanayi, kalubale ne da duk fadin duniya ke fuskanta. Ya ce ya yi imanin cewa, taron zai samar da kyakkyawar dama ga kamfanoni da kungiyoyin masana na larduna da biranen kasashen biyu, bisa manufar kiyaye hadin kansu sosai.

Yayin taron, Sin da Amurka sun gabatar da jerin sakamakon da suka samu, ciki hadda hadin kansu a fannonin samun ci gaba ba tare da fitar da iska mai dumamma yanayi ba, da karkata hanyar samun ci gaba mai kare muhalli, da mu’ammalar matasa da sauransu. Daga cikinsu, kafar CGTN daga babban rukunin CMG da kwalejin binciken sauyin yanani tsakanin California da Sin, za su hada gwiwa wajen gabatar da shirin talibijin mai taken “Tattaunawa kan sauyin yanayi a tsakanin gabobi biyu na tekun Pacific”, da zummar kara fahimtar juna da gabatar da dabarun kirkire-kirkire don tinkarar matsalar sauyin yanayi. (Amina Xu)