logo

HAUSA

Shugaba Bassirou Diomaye Faye na kasar Senegal ya kai ziyarar aiki da sada zumunta a kasar Mali

2024-05-31 09:32:25 CMG Hausa

Shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Kanal Assimi Goita ya tarbi takawaransa na kasar Senegal a ranar jiya Alhamis 30 ga watan Mayun shekarar 2024, a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Modibo Keita-Senou dake birnin Bamako, sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye, da ya kai ziyarar aiki da sada zumunta a kasar Mali.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya turo mana da wannan rahoto. 

Shi dai wannan rangadi shi ne na farko a kasar Mali, tun bayan zabensa a kan karagar mulkin kasar Senegal a karshen watan Maris din shekarar 2024.

Ita dai wannan ziyara na da manufar karfafa dankon zumunci da tarihin makwabtaka mai kyau, da abokantaka da sada zumunta, tare da kuma yaukaka huldar dangantaka a fannoni daban daban na ci gaban kasa da suka hada da tattalin arziki, siyasa, ilimi, kasuwanci, tsaro, da na al’umma da ke tsakanin kasashen biyu.

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyar Nijar.