logo

HAUSA

Mataimakin ministan harkokin wajen Sin ya gana da mai ba da taimako ga mataimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa

2024-05-31 14:08:08 CMG Hausa

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu ya yi sahihiyar tattaunawa mai zurfi, kan huldar dake tsakanin Sin da Amurka da batutuwan duniya dake jan hankalin kasashen biyu da mai ba da taimako na farko ga mataimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa, Jonathan Finer.

Bangarorin biyu suna ganin cewa, ya kamata a ci gaba da aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito a yayin ganawarsu a birnin San Francisco, da kara yin mu’amala a tsakanin manyan jami’an kasashen biyu, da fadada hadin gwiwa, da daidaita matsaloli, da kokarin raya huldar dake tsakanin Sin da Amurka. Ma Zhaoxu ya yi bayani game da matsayin Sin kan batun yankin Taiwan da yankin kudancin tekun kasar Sin, ya kuma jaddada cewa, ya kamata Amurka ta dauki matakai don cika alkawarin shugaban kasar Joseph Biden, da girmama moriyar ikon mallakar kasar Sin a fannin tsaro da samun bunkasuwa. (Zainab Zhang)