logo

HAUSA

An gudanar da taron tattaunawa mai taken “Sin da Duniya: Yin hadin gwiwa da tinkarar kalubale da kuma samun moriyar juna”

2024-05-31 13:52:54 CMG Hausa

Yayin cika shekaru 3 da jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping game da inganta aikin watsa labaru a kasa da kasa, an gudanar da taron tattaunawa mai taken “Sin da Duniya: Yin hadin gwiwa da tinkarar kalubale da kuma samun moriyar juna” a jiya Alhamis a nan birnin Beijing, inda shugaban babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

A cikin jawabinsa, Shen Haixiong ya bayyana cewa, a shekarun baya baya nan, CMG ya yi kokarin yin kirkire-kirkire kan harkokin diplomasiyya ta hanyar watsa labaru, wanda ya kafa jerin tsarin hadin gwiwa tsakaninsa da kafofin watsa labaru na kasa da kasa. Ya kara da cewa, CMG yana son koyon fasahohi daga kafofin watsa labaru abokan hulda na kasa da kasa, don kirkiro kyakkyawar makoma tare.

A gun taron, an gabatar da takardar binciken ra’ayoyin jama’ar duniya game da hadin gwiwa da tinkarar kalubale da kuma samun moriyar juna a tsakanin Sin da duniya, wadda kwalejin nazarin ilmin watsa labaru a kasa da kasa a sabon zamani ya gabatar. Bisa binciken da aka yi, an ce, kashi 85.3 cikin dari na wadanda suka amsa tambayoyi sun amince da tunanin hanyar siliki na Sin wato hadin gwiwa cikin lumana, da bude kofa ga kasashen waje, da amincewa da bambance-bambance, da koyi da juna, da kuma samun moriyar juna. (Zainab Zhang)