Ba za a iya rasa adalci wajen warware matsalar Falasdinu ba
2024-05-31 21:57:48 CMG Hausa
Jiya Alhamis, 30 ga watan Mayu, yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza da ke da nisan dubban kilomita daga birnin Beijing, taron ministoci karo na 10 na dandalin tattauna hadin-kan Sin da kasashen Larabawa, ya fitar da hadaddiyar sanarwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa kan batun Falasdinu, inda suka fitar da wata murya, don sa kaimi ga warware rikicin Gaza cikin gaggawa da kuma warware matsalar Palasdinu cikin adalci, da samar da mafita mai dorewa.
Yayin da yanayin da ake ciki tsakanin Falasdinu da Isra'ila ke kara tabarbarewa, taron ministocin karo na 10 na dandalin tattauna hadin-kan kasar Sin da kasashen Larabawa ya gabatar da kira mafi girma na tsayawa tsayin daka kan mara baya ga al'ummar Palasdinu wajen maido da hakkinsu na kasa baki daya, wadda ta samu kulawa sosai daga wajen kasashen duniya.
"Yaki ba zai iya ci gaba da wanzuwa har abada ba, ba za a rasa adalci har abada ba, kuma ba za a iya girgiza shirin 'kasashen biyu' ba", shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya bayyana haka a cikin muhimmin jawabin da ya gabatar a bikin bude wannan taro, wanda ya ja hankalin jama’a.
Batun Falasdinawa dai shi ne jigon batun Gabas ta Tsakiya. Ko yaya yanayin kasa da kasa ya canza, kasar Sin tana goyon bayan maido da halaltaccen hakkin al'ummar Palasdinu. Za kuma ta ci gaba da tsayawa tare da kasashen Larabawa, da tabbatar da adalci, da kokarin ganin an tsagaita bude wuta ba tare da wani sharadi ba cikin gaggawa tsakanin Falasdinu da Isra'ila, kana da inganta warware rikicin Palasdinu cikin daidaito da adalci da zai dore, da samar da zaman lafiya na hakika a yankin Gabas ta Tsakiya da ke cikin mawuyacin yanayi sakamakon yaki. (Bilkisu Xin)