logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Tunisia Kais Saied

2024-05-31 11:46:56 CMG Hausa

Da safiyar yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Tunisia Kais Saied, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. Shugaba Kais Saied na ziyara a kasar Sin, tare da halartar bikin bude taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa karo na 10.

A yayin tattaunawar, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Tunisia, bangarorin biyu sun kiyaye girmama juna da tabbatar da adalci a tsakaninsu da kuma goyon baya juna, lamarin da ya kai su ga rubuta babin nuna goyon bayan juna tsakanin kasashe masu tasowa.

A nasa bangare, shugaba Saied ya bayyana cewa, huldar dake tsakanin Tunisia da Sin tana da inganci, domin kasashen biyu suna bin ka’idoji iri daya, haka kuma suna da burin iri daya, kana suna kokari tare don samar da kyakkyawar makomar dan Adam. 

Bayan tattaunawar, bangarorin biyu sun gabatar da hadaddiyar sanarwa kan raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.(Zainab Zhang)