logo

HAUSA

Wang Yi ya yi jawabi ga dandalin koli na masanan Sin da Rasha

2024-05-31 14:20:44 CMG Hausa

 

Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS kana ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya jaddada cewa, Sin za ta hada gwiwa da Rasha bisa manyan tsare-tsare a matakin koli, domin amfanawa al’umommin kasashen biyu, da taka karin rawar gani ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya.

Wang Yi ya bayyana haka ne a jiya Alhamis, yayin da yake jawabi ga taron dandalin koli na masanan Sin da Rasha ta kafar bidiyo.

Ban da wannan kuma ya gabatar da wasu shawarwari biyar kan hadin kan bangarorin biyu. Na farko, mara wa juna baya kan hadin gwiwar samun ci gaba da kuma farfadowa, na biyu cimma moriya tare bisa hadin kai da bude kofa, na uku, inganta huldar al’umommin biyu ta hanyar kara mu’ammala da koyi da juna, kana na hudu, jagorantar aikin daidaita harkokin duniya bisa nauyin dake wuyansu, kana na karshe shi ne, shiga harkokin kasa da kasa bisa matsayin adalci. (Amina Xu)