Li Qiang ya mika sakon murna ga sabon firaministan kasar Chadi
2024-05-31 15:09:28 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya taya Allah-Maye Halina murnar zama sabon firaministan kasar Chadi.
A cikin sakon taya murnar da ya aike masa a jiya, Li Qiang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana bayar da muhimmanci matuka ga raya dangantakar dake tsakaninta da Chadi. Kuma yana son yin kokari tare da firaminista Halina wajen zurfafa imani da juna a fannin siyasa da fadada hadin gwiwarsu, ta yadda za a inganta dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. (Zainab Zhang)