logo

HAUSA

Ministocin tsaron Sin da Amurka sun gana a kasar Singapore

2024-05-31 15:14:38 CMG Hausa

A yau Juma’a, ministan tsaron kasar Sin janar Dong Jun ya gana da takwaransa na kasar Amurka Lloyd Austin a yayin taron tattaunawa na Shangri-la da ake gudanarwa a kasar Singapore.

A kuma yau din, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian ya yi bayani game da ganawar, yayin taron manema labaru da aka gudanar a kasar Singapore, inda ya ce ministocin biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan huldar dake tsakanin Sin da Amurka, da yankin Taiwan, da kuma tekun kudancin kasar Sin. (Zainab Zhang)