logo

HAUSA

Xi Jinping ya jaddada muhimmancin raya dukkan harkokin da suka shafi yara

2024-05-31 20:16:02 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nanata muhimmancin raya dukkan harkokin da suka shafi yara ta kowacce fuska, a cikin amsar wasikar daliban wata makarantar firamare dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar.

Xi Jinping ya kuma karfafawa daliban gwiwar zama masu dogaro da kansu kuma yara masu kyakkyawan buri a sabon zamani dake kaunar kasarsu da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Cikin wasikar, Xi Jinping ya kuma mika gaisuwar ranar yara ta duniya ga dukkan yaran dake fadin kasar.

A baya-bayan nan ne dalibai daga makarantar firamare ta Zhijiang dake lardin Sichuan, suka rubuta wasika ga shugaba Xi, inda suka masa bayani game da yanayin karatu da rayuwarsu.

A cewar Shugaba Xi, yara su ne makomar kasar, yana mai karfafa musu gwiwar zama masu basira da za su iya daukar nauyin gina kasa mai karfi da cimma burin farfado da kasar. (Fa’iza Mustapha)