logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya zartas da kuduri game da yanayin Rafah cikin hanzari

2024-05-30 10:57:40 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Sin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga dukkan kasashe membobin kwamitin sulhu na MDD, da su yi watsi da yunkurin siyasa, da sanya rayuwar jama’a a gaban komai, su zartas da wani kudurin kai dauki ga yanayin Rafah na zirin Gaza cikin hanzari.

Fu Cong ya bayyana haka ne jiya, a gun taron kwamitin sulhu na MDD kan batun Palesdinu da Isra’ila, inda ya ce an shafe lokaci mai tsawo, kasa da kasa suna maida hankali sosai kan yanayin da ake ciki a yankin Rafah, da yin kira da a tsagaita bude wuta a yankin ba tare da bata lokaci ba. Ya ce sau da dama kuma, kwamitin sulhu ya tattauna kan wannan batu, tare da kiran kada a kai hari yankin Rafah. Haka zalika, kotun duniya ta gabatar da umurnin daukar matakai, wato ta bukaci Isra’ila ta bi yarjejeniyar magance aikata laifin kare-dangi, da dakatar da kai hare-hare yankin Rafah. Amma Isra’ila ta yi watsi da kiraye-kirayen kasa da kasa game da wannan batu, inda ta kai hare-hare sansanonin ‘yan gudun hijira fiye da 10 a zirin Gaza, wadanda suka haddasa mutuwar fararen hula masu yawa. Lamarin da kasar Sin ke Allah wadai da shi. (Zainab Zhang)