logo

HAUSA

Sin na goyon bayan WHO ta ci gaba da jagorantar yarjejeniyar tunkarar annoba

2024-05-30 12:26:29 CMG Hausa

Kasar Sin na fatan hukumar lafiya ta duniya (WHO) za ta ci gaba da jagorantar tattaunawa game da yarjejeniyar tunkarar annoba.

Hu Guang, shugaban hukumar kandagarki da takaita cututtuka ta kasar Sin (NDCPA) ne ya bayyana haka a Talata 28 ga wannan wata. A cewarsa, yarjejeniyar wani muhimmin bangare ne na yi wa tsarin jagorantar kiwon lafiyar al’ummar duniya a nan gaba garambawul.

Da yake hira da manema labarai a jiyan, Hu Guang ya ce kasar Sin tana shiga ana damawa da ita a cikin tattaunawar, inda take taka muhimmiyar rawa wajen tsara daftarin yarjejeniyar. (Fa’iza Mustapha)