‘Yancin Taiwan na nufin yaki, in ji kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin
2024-05-30 21:43:59 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya ce ‘yancin yankin Taiwan na nufin barkewar yaki, kuma dunkulewar sassan kasar Sin matakin tarihi ne da ba zai yiwu a mayar da shi baya ba.
Wu Qian, ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da ya gudanar, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa mai nasaba da kalaman da jagoran yankin na Taiwan Lai Ching-te ya yi yayin rantsuwar kama aiki.
Wu ya kara da cewa, kalaman Lai a yayin rantsuwar sun shaida karara yadda yake kokarin neman ‘yancin yankin Taiwan da karfin tuwo, tare da dogaro ga wasu sassan ketare. To sai dai kuma rundunar sojojin kasar Sin PLA, na matukar adawa da hakan, ta kuma mayar da martani da matakai masu karfin gaske. (Saminu Alhassan)