logo

HAUSA

Isra’ila ta kwace iko da iyakar Gaza da Masar yayin da take kara kutsawa Rafah

2024-05-30 12:36:14 CMG Hausa

Dakarun Isra’ila sun kwace iko da wani yanki da ba a yaki dake kan iyakar zirin Gaza da Masar, lamarin da ya ba Isra’ila cikakken iko da baki dayan iyakar kasa na yankin Palasdinu.

Isra’ila na ci gaba da kai munanan hare-hare Rafah dake kudancin Gaza duk da umarnin da kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ta bayar, na a dakatar da kai hare-hare birnin, inda rabin al’ummar Gaza miliyan 2.3 suka samu mafaka a baya.

Cikin wani jawabi ta talabijin, kakakin rundunar sojin Isra’ila Daniel Hagari, ya ce dakarun Isra’ila sun samu iko da mashigar Philadelphi, yana mai amfani da sunan da rundunar sojin Isra’ila ke kiran mashigar mai tsawon kilomita 14, dake yankin iyaka daya tilo tsakanin zirin Gaza da Masar. (Fa’iza Mustapha)