Yunnan: Akwai Wata Makarantar Firamare Ta Zumuncin Sin Da Equatorial Guinea
2024-05-30 16:12:19 CMG Hausa
Masu kallonmu, barka da war haka. Kwanan baya, shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya kawo ziyarar aiki karo na 11 a kasar Sin. Yayin ziyarar, ya yi hira ta kafar bidiyo da daliban wata makarantar firamare dake lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin, wadda ta nuna kyakkyawan zumuncin dake tsakanin Sin da Equatorial Guinea.