logo

HAUSA

Mashirya gasar Olympic ta Paris ta 2024 sun fitar da tsarin dandamalin karbar kyaututtuka a yayin gasar

2024-05-30 19:42:38 CMG Hausa

Mashirya gasar Olympic ta birnin Paris ta 2024, sun fitar da tsarin suffar dandamalin karbar kyaututtuka da za a lashe a yayin gasar dake tafe. An fitar da surar dandamalin ne a helkwatar kwamitin shirya gasar.

Kamar dai lambobin karramawa da za a lashe, shi ma suffar dandamalin na kama da babbar hasumiyar birnin wato “Eiffel Tower”, mai karafa a gefen waje na dandamalin.

An kuma kawata dandamalin da launukan fari da toka-toka, kana an kera dandamalin da katako, da kaso 100 bisa dari na kayayyakin roba da ake iya sabunta amfani da su, da kuma tsarin kira mai girma daban daban gwargwadon yanayin ‘yan wasan da za su yi amfani da shi.

Ga misali, dandamali mafi karancin tsayi, domin ‘yan wasa masu gudanar da gasanni na daidaiku, na kunshe da mabanbantan girma 3, yana kuma da matsakaicin tsayi na mita 4. Dandamalin ‘yan wasan kwallon kafa shi ne mafi tsayi, inda zai iya daukar ‘yan wasa 43, yana kuma da tsayin sama da mita 40.

Ko wane dandamali na da nauyin kimanin kilogiram 45. Mashirya gasar ta Paris sun tsara amfani da dandamali masu mabanbantan girma har 685, inda aka ajiye guda 45 domin jiran ko ta kwana.

Da yake tsokaci kan hakan, shugaban kwamitin tsara gasar Tony Estanguet, ya ce dandamalin ba da lambobin yabo muhimmin jigo ne na auna nasara, da murnar kammala gasa. Ga ‘yan wasan Olympic da takwarorin su masu wasa ajin masu bukata ta musamman, kaiwa ga dandamali na nuna cimma nasara. Shi ne ke nuna an kawo karshen doguwar tafiya.

An tsara cewa, ‘yan wasa da suka lashe lambobin zinari za su tsaya kan dandamali mai tsayin santimita 35, yayin da wadanda suka lashe azurfa da tagulla za su tsaya kan dandamali mai tsayin santimita 20.

Za a yi amfani da wannan salo ga ‘yan wasa na ajin masu bukata ta musamman, sai dai a wannan aji dukkanin ajin masu karbar lambobin yabon uku za su tsaya ne kan dandamali mai tsayin santimita 20, wanda aka yi shi da gangara ta wurin hawa da keyen guragu.