Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na UAE Mohammed Bin Zayed al-Nahyan
2024-05-30 20:14:04 CMG Hausa
Da yammacin yau Alhamis 30 ga wata, a babban dakin taron al’umma dake birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa wato UAE, Mohammed Bin Zayed al-Nahyan, wanda har yanzu ke ziyarar aiki a kasar Sin, ya kuma halarci bikin bude taron ministoci karo na 10, na dandalin tattauna hadin-kai tsakanin Sin da kasashen Larabawa.
A yayin ganawar, Xi Jinping ya nuna cewa, kasashen yankin Gabas ta Tsakiya wani muhimmin bangare ne na kasashe masu tasowa, kuma suna da karfi a fannin mayar da duniya ta zama mai bangarori da dama. Kasar Sin tana goyon-bayan kasashen yankin, wajen ci gaba da bin hanyar samun bunkasuwa mai dacewa da yanayinsu, da kuma tsayawa tsayin daka kan hanyar hadin kai, da dogaro da kai, da zaman lafiya da kuma sulhu, tare kuma da dagewa wajen kawar da bambance-bambance ta hanyar tuntubar juna, da rike makomarsu a hannunsu.
A cewar shugaba Xi, kasarsa tana son yin hadin gwiwa tare da Hadaddiyar Daular Larabawa, da sauran kasashen Larabawa, don samun nasarar karbar bakuncin taron koli na biyu na Sin da kasashen Larabawa, da sa kaimi ga gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga Sin da kasashen Larabawa.
A nasa bangaren kuwa, shugaba Mohammed ya bayyana cewa, kasarsa tana mai da hankali sosai kan raya dangantakar da ke tsakaninta da kasar Sin, tana kuma son amfani da bikin cika shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, a matsayin wata dama ta kara zurfafawa, da fadada hadin gwiwa a fannoni daban daban, ciki har da tattalin arziki da cinikayya, da zuba jari, da makamashi, da kimiyya da fasaha, da ilimi, da al'adu da dai sauransu.
Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu sun ganewa idannunsu yadda aka rattaba hannu, kan wasu takardun hadin gwiwa da suka shafi zuba jari, da gina shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kimiyya da fasaha, da yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, da koyar da harshen Sinanci, da yawon bude ido da sauran fagage.
Kafin shawarwarin, shugaba Xi ya shirya wani biki a wajen babban dakin taron al’ummar, don maraba da zuwan shugaba Mohammed, kana a daren ranar, ya shirya masa liyafa a wurin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)