Babban hafsan tsaron Najeriya ya karbi bakuncin mataimakin babban hafsan sojojin sama na kasar China
2024-05-30 09:54:47 CMG Hausa
Babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa ya karbi bakuncin mataimakin babban hafsan sojin sama na kasar China Lutanal Janar Jia Zhigang a hediwkatar tsaron Najeriya dake birnin Abuja.
Lutanal Kanal Jia ya zo Najeriya ne bisa amsa gayyatar da babban hafsan sojin sama na Najeriya ya yi masa domin halartar bikin cika shekaru 60 da samuwar rundunar sojin saman Najeriya.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron Najeriya Birgediya Janaral Tukur Gusau wadda kuma aka karba manema labarai jiya Laraba 29 ga wata, ta ambato mataimakin babban hafsan sojin sama na kasar China Liftanal Janaral Jia Zhigang yana yabawa kokarin dakarun sojin saman Najeriya wajen yaki da ayyukan ’yan ta’adda da kuma shawo kan matsalolin hare-haren ’yan ta’addan.
Liftanal Janaral Jia ya jaddada muhimmancin hada kai da juna wajen ayyukan bincike da kirkire-kirkire da bunkasa fasahar sarrafa jiragen yaki mara matuki kana da horas da kananan dakarun sojin sama.
Ya ce kasar China a shirye take da kara kyautata alakar harkokin tsaro da Najeriya domin yakar ayyukan ta’addanci a kowanne sashe.
A jawabinsa babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa ya yaba matuka bisa wannan ziyara ta jami’an rundunar sojin saman kasar China, tare da bayyana godiya a game da yadda kasar China ke baiwa Najeriya taimako da goyon bayan wajen yaki da ’yan ta’adda. (Garba Abdullahi Bagwai)