logo

HAUSA

Rundunar PLA za ta shiga atisayen hadin gwiwa a Najeriya

2024-05-30 20:05:31 CMG Hausa

Kakakin rundunar sojin kasar Sin PLA Wu Qian, ya ce jirgin ruwan yaki na rundunar sojojin ruwan kasar Sin mai suna Xuchang, zai shiga atisayen hadin gwiwa a yankin tekun Najeriya.

A cewar jami’in, jirgin Xuchang na cikin jiragen ruwan rundunar PLA da a yanzu ke rakiyar jiragen ruwa a mashigin tekun Aden, da yankin tekun Somalia, don gudanar da aikin ba da kariya ga jiragen ruwa da ke zirga zirga a yankin karo 46.

Wu Qian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a ma’aikatar tsaron kasar Sin a yau Alhamis, ya ce atisayen zai mayar da hankali ga yaki da ‘yan fashin teku, da barayin danyen mai, zai kuma kunshi ayyukan sintiri da sadarwa na hadin gwiwa.

Kaza lika, jami’in ya ce shigar sojojin ruwan rundunar PLA wannan atisaye, zai taimaka wajen zurfafa musaya tsakanin dakarun soji, da aiwatar da hadin gwiwa na zahiri tsakanin Sin da sauran kasashe masu alaka da hakan, kana zai ingiza gina babban tsari na samar da al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya. (Saminu Alhassan)