Wang Yi ya gana da manyan jami’an kasashen da suke halartar dandalin tattauna hadin kan Sin da kasashen Larabawa
2024-05-30 13:34:03 CMG Hausa
Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da manyan jami’an wasu kasashen Larabawa, wadanda suke halartar taron dandalin tattauna hadin kan Sin da kasashensu.
Yayin da yake ganawa da firaminista, kana ministan harkokin wajen kasar Libya Abdul Hamid Dbeibah, Wang Yi ya ce, Sin tana goyon bayan kasar wajen samun bunkasuwa mai dorewa da ikon mulki da cikakken yankin kasar da ma mika mulki a siyasance bisa ka’idar dogaro da karfi da moriyar jama’ar kasar. A nasa bangare, Abdul Hamid Dbeibah ya ce, Libya na dora muhimmanci kan huldar dake tsakanin kasashen biyu, kuma kasar na nacewa ga manufar “kasar Sin daya tak a duniya”. Yana mai fatan Sin za ta taka rawar gani wajen magance batun Palasdinu.
A lokacin da Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Mauritania Salem Ould Merzoug, ya ce, Sin za ta ci gaba da goyon bayan kasar wajen bin hanyar da ta dace da halin da take ciki da kin yarda da karfin waje ya tsoma baki cikin harkokin gidanta. A nasa bangare kuwa, Merzoug ya ce, kasarsa na tsayawa kan manufar “kasar Sin daya tak a duniya” ba tare da tangarda ba, kuma yana fatan hadin gwiwa da Sin don gaggauta bunkasa huldar dake tsakanin kasashen Larabawa da Afrika da Sin, da ingiza raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya.
Ban da wannan kuma, Wang Yi ya gana da takwaransa na Aljeriya Ahmed Attaf, inda ya ce, Sin na fatan za su ci gaba da goyon bayan juna da hadin kai don kiyaye adalci da daidaiton duniya da muradun kasashe masu tasowa. Shi kuwa Ahmed Attaf cewa ya ce, a ko da yaushe, Aljeriya na amincewa da ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”, kuma yana fatan kara hadin gwiwa da Sin a dukkan fannoni, tare da zurfafa huldarsu.
Har ila yau, Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Moroco Nasser Bourita, inda ya ce, Sin na fatan zurfafa hadin kai da kasar a fannin tattalin arziki da cinikayya da zuba jari da masana’antu da yawon shakatawa da sufurin fasinjoji da dai sauransu, da kuma aza tubali mai inganci ga huldar jama’ar kasashen biyu don kafa wata hanya ta samun makoma mai haske wajen raya huldar abota bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu. Bourita a nasa bangare ya ce, Moroco na daukar huldarta da Sin da muhimmanci matuka, kuma ba za ta sauya matsayin da take dauka na yarda da manufar “kasar Sin daya tak a duniya” ba, yana mai fatan zurfafa hadin kai da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu karkashin wannan dandali da ma dandalin tattauna hadin kan Sin da Afrika. (Amina Xu)