Masana a Afrika sun tattauna kan manufofin haraji na nahiyar
2024-05-30 12:42:46 CMG Hausa

Masana a nahiyar Afrika sun hadu a birnin Nairobin Kenya a jiya Laraba, domin tattauna dabarun inganta tara kudin shiga, ta hanyar ingantattaun matakan haraji a nahiyar.
Taron karawa juna sani kan haraji karo na 9 na shekarar 2024 na tsawon yini 3, ya hallara wakilai sama da 200, cikinsu har da masu kula da harkokin haraji da abokan hulda, domin shawo kan muhimman batutuwa game da haraji, kamar kudin shigar da ake samu daga cinikayya tsakanin kasa da kasa. (Fa’iza Mustapha)
