logo

HAUSA

Ministan ma'adinan kasar Bénin da ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Yamai bai samu ganawa ba da shugaban kasar Nijar

2024-05-30 09:56:41 CMG Hausa

Ministan ma'adinan kasar Bénin ya kawo wata ziyarar aiki a ranakun Litinin da Talata a birnin Yamai domin ganawa da hukumonin Nijar domin neman warware bakin zare game da rikicin diplomasiyya dake tsakanin kasashen tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Julin shekarar 2023 a kasar Nijar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Maman Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

 

A yayin taron manema labaru a ranar 28 ga watan Mayun shekarar 2024 a birnin Cotonou na kasar Bénin, ministan ma'adinan kasar Samou Seidou Adambi ya shaidama 'yan jarida na gida da na waje cewa ya kai wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a birnin Yamai na kasar Nijar rike da sakon shugaban kasar Bénin Patrice Talon zuwa ga takwaransa na kasar Nijar birgadiye janar Abdourahamane Tiani domin daidaita rikicin diplomasiyya dake tsakanin kasashen biyu. Sai dai, a cewarsa, duk da kokarin da shugaba Patrice Talon yake yi ta hanyar rubuta wasikar zuwa ga shugaban kasar Nijar, domin sulhunta wannan takkadama, hakan ya tityra domin shugaba Abdourahamane Tiani ya ki ya gana da manzon musamman da shugaban Bénin ya turo a birnin Yamai, in ji minista Samou Seidou Adambi.

Ministan ma'adinan kasar Bénin ya bayyana cewa, ya samu ganawa da sauran jami'ai kamar takwaransa na ma'adinai da kuma shugabannin kwastan na kasar Nijar game da batutuwan ficewar man fetur din Nijar zuwa tashar ruwan Sème, da kuma yadda da za'a kawo karshen matsalolin jigilar dayen man fetur din Nijar zuwa kasar Bénin da mafitarsa daga kasar.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna ta yi tsami bayan biyo al'amuran ranar 26 ga watan Julin shekarar 2023 da kuma takunkumin kungiyar CEDEAO da na UEMOA da ma yunkurin matakin soja kan Nijar da kasar Bénin ta nuna zakewa. Da kuma yadda kasar Bénin ta amince da sojojin Faransa su tare kasarta bayan an kore su daga kasar Nijar.

Hakazalika, duk da cewa, kasar Benin ta bude iyakokinta da kasar Nijar, amma har yanzu a bangaren Nijar iyakoki suna rufe da kasar Bénin. Lamarin da ya janyo matsalolin kasuwanci da shige da ficen dukiyoyi da na al'umomi tsakanin kasashen biyu.

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyar Nijar.