An fara kada kuri’u a babban zaben Afirka ta kudu
2024-05-29 19:52:57 CMG Hausa
Da safiyar yau Laraba ne al’ummun Afirka ta kudu suka fara kada kuri’u, a babban zaben kasar na bana. Sama da ‘yan kasar miliyan 27 ne ake sa ran za su yi zabe a cibiyoyin kada kuri’a sama da 23,000, don zabar sabbin ‘yan majalissun dokokin kasa, da na larduna, kamar dai yadda hukumar zaben kasar mai zaman kan ta IEC ta tabbatar.
Zaben ‘yan majalissun dokokin kasa, da na lardunan kasar na shekarar 2024, ya zo daidai lokacin da kasar ke bikin ciki shekaru 30 da samun ‘yancin kai, da komawa mulkin dimokaradiyya, kuma wannan ne karo na 7 da kasar ke gudanar da babban zabe, tun bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata a kasar a shekarar 1994.
Hukumar IEC ta ce za a sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi. Daga bisani kuma sabuwar majalissar dokokin kasar za ta zabi shugaban kasa, wanda zai jagoranci Afirka ta kudun a tsawon shekaru 5 masu zuwa. (Saminu Alhassan)