logo

HAUSA

Manufar Sin daya tak a duniya ba za ta taba sauya ba

2024-05-29 08:11:19 CMG Hausa

A baya bayan nan babban taron hukumar lafiya ta duniya ko WHA karo na 77 ya yi watsi da shawarar da wasu kasashe suka gabatar masa, na wai a baiwa yankin Taiwan damar halartar taron a matsayin mai sa ido.

Gamayyar kasashen da suka nuna adawa da wannan shawara, sun wakilci bakin daukacin sassan kasa da kasa, kana sun tabbatar da ingancin manufar Sin daya tak a duniya, wadda ta zamo manufa da ba za a iya kawar da ita ba.

Da wannan mataki na mahalarta taron WHA na bana, sau 8 ke nan a jere, ana yin watsi da waccan shawara ta baiwa yankin Taiwan gayyatar halartar wannan taro, don haka dai ma iya cewa duniya ta amsa manufar kasar Sin daya tak a duniya, a matsayin manufar da ba za su juya mata baya ba.

Har ila yau, matakin watsi da wannan shawara da kasashe mahalarta taron na WHA suka dauka, na watsi da waccan shawara na nuna duk wani yunkuri da wasu ’yan amshin-shata za su yi, na shigar da mummunan ra’ayin wasu kasashe cikin taron WHA, zai gamu da koma baya. Duba da cewa tun a shekarar 1992, aka cimma daidaito tsakanin mahalarta taron na WHA na wancan lokaci, cewa kasar Sin daya ce tak a duniya.

Kamar dai yadda kasar Sin ta sha fada tun a baya, Sin daya ce tilo a duniya, kuma yankin Taiwan bangare ne na kasar Sin da ba za a taba balle shi ba. Kuma gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ita ce halastacciyar gwamnati dake wakiltar daukacin kasar jama’ar Sin a duniya. Kana a zahiri take cewa, wannan manufa na da karfin da ba abun da zai iya girgiza ta. 

A daya bangaren kuma, babban yankin Sin zai ci gaba da aiwatar da muhimman matakai, ciki har da tsara tawagar kwararru a fannin kiwon lafiya, wadda za ta rika halartar taron hukumar lafiya ta duniya WHO, tare da sanar da yankin Taiwan duk wasu batutuwa na gaggawa a fannin kiwon lafiya da WHO ta fadakar a kan su ba tare da bata lokaci ba. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Faeza Mustapha)