logo

HAUSA

Rahoto kan yadda aka keta hakkin dan Adam a kasar Amurka a shekarar 2023

2024-05-29 16:21:20 CMG Hausa

A ranar Laraba 29 ga watan Mayun nan, ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin ya gabatar da rahoto kan laifuffukan keta hakkin dan Adam da kasar Amurka ta aikata a shekarar 2023.

A cikin rahoton, an ce, yanayin hakkin dan Adam a kasar Amurka ya ci gaba da lalacewa a shekarar 2023 da ta gabata, inda gibin da ake samu tsakanin al’ummun kasar ke kara habaka. An ce, yayin da mutane kalilan ke mallakar ikon sarrafa harkokin siyasa da tattalin arziki, gami da zaman al’umma a kasar, yawancin jama’ar kasar na ta fama da matsalar rashin damar tabbatar da ’yanci da kare hakkinsu na tushe. Wannan yanayi ya sa kaso 76% na al’ummar Amurka na ganin hanyar raya kasar na kan kuskure.

A kasar Amurka, jam’iyyun siyasa na gudanar da mummunar takara, lamarin da yake hana gwamnatin kasar sauke cikakken nauyin dake bisa wuyanta na gudanar da mulki, da kare hakkin jama’a, musamman ma hakkinsu ta fuskar siyasa. Sa’an nan yadda jam’iyyun siyasa guda 2 na kasar suka kasa cimma matsaya kan batun takaita bindigogi, ya sa ana ta samun abkuwar manyan hare-haren bindiga a kasar, abin da ya haddasa rasa rayukan mutane kimanin dubu 43 a kasar a shekarar 2023, wato mutane 117 a kowacce rana bisa matsakaicin mataki. 

Ban da haka, ’yan sandan kasar Amurka suna amfani da karfin tuwo yadda suka ga dama, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 1247 a shekarar 2023 da ta gabata, adadin da ya kai matsayin koli tun daga shekarar 2013. Sai dai duk da haka, kusan ba a taba aiwatar da tsarin hukunta ’yan sanda masu laifi ba. A halin yanzu, yawan al’ummar kasar Amurka bai kai kaso 5% na adadin daukacin al’ummar duniya ba, amma yawan ’yan zaman kaso na kasar ya kai kashi 25% cikin na jimillar na duniya baki daya. Ta haka za a iya ganin yadda kasar ta cancanci lakabin “kasar gidajen kaso”.

A nasu bangare, jam’iyyun siyasan kasar sun yi ta kokarin takara da juna ta wata mummunar hanya, inda suke amfani da tsarin raba yankunan zabe wajen sarrafa sakamakon zabuka, lamarin da ya haddasa matsalar kasa fitar da kakakin majalissar wakilai ta kasar har sau 2. Ganin haka ya sa amanar da jama’ar kasar ke dora wa gwamnati dada raguwa, har ma jimillar ma’aunin shaida imanin da jama’ar kasar suke nuna wa gwamnatin tarayya ta tsaya kan kaso 16% kacal.

Manufar bambancin launin fata da ta dade tana addabar al’ummar Amurka ta tsananta sosai. Masanan MDD sun bayyana cewa, wannan manufar nuna bambancin launin fata na Afirkawa ta kawo illa ga rundunar ’yan sanda, da tsarin doka da shari’a. Ban da wannan kuma, saboda yadda ake nuna bambancin launin fata a fili a bangaren kiwo lafiya, yawan rasuwar mata bakaken fata masu juna biyu ya ninka har sau 3 bisa na fararen fata. Kaza lika yawan ’yan Asiya da suke fama da wannan matsala ya kai kashi 60%. Sannan kuma “Shiri addabar kasar Sin” da aka fitar domin cin zarafin masu kimiyya da fasaha masu asalin kasar Sin na haifar da babbar barazana. Shi ya sa, Amurka ta zama kasa mafi tsattsauran ra’ayi a bangaren launin fata, har ra’ayin ya yi saurin bazuwa zuwa sauran kasashe ta kafofin shafunan sada zumunta, da kide-kide, da wasannin kwamfuta da sauransu.

Har ila yau, Amurka na fama da gibin matalauta da masu wadata mai zurfi, inda wasu masu ayyukan yi ba sa samun isassun kudaden shiga, kuma tsarin ba da tabbaci ga tattalin arzikin, da zaman rayuwar jama’a ba shi da isashen karfi cikin dogon lokaci. Ban da wannan kuma, Amurkawa sun dade suna fama da gibin kudin shiga ba bisa ka’ida ba, shi ya sa gibin ya kai matsayin mafi tsanani tun daga lokacin barkewar babban rikicin tattalin arziki a shekarar 1929. Amurka na da iyalai marasa isassun kudin shiga miliyan 11.5, amma gwamnatin ba ta daga ma’aunin kudin shiga mai tushe tun daga shekarar 2009. 

A shekarar 2023, darajar kudin kasar dalar 1 ya ragu da kashi 70% bisa na makamancin lokaci a 2009. Sakamakon haka, iyalan da ba su da isashen kudin shiga, ba su iya biyan bukatunsu na sayen abinci, da hayar gidaje, da sayen makamashi da sauransu ba. Har ila yau, Amurkawa da ba su da gidajen kwana ya zarce dubu 650, adadin ya kai matsayin koli a cikin shekaru 16 da suka gabata. “Mafarkin Amurka” ya rushe, saboda masu aiki suna fuskantar karancin kudin shiga, dalilin da ya haddasa barkewar yajin aiki a shekarar 2023, wanda ya kasance irinsa mafi girma a karni na 21.

Bugu da kari, a cikin dogon lokacin da ya gabata, an keta hakkin yara da mata a kasar Amurka, kuma, ba a yi amfani da dokar kare adalcin jinsi yadda ya kamata ba. Ya zuwa yanzu, kasar Amurka ba ta zartas da “yarjejeniyar kawar da bambancin ra’ayin da ake nuna wa mata ba” wadda MDD ta tsara. Haka kuma, kawo yanzu kasar Amurka ita ce kasa kadai cikin mambobin MDD da ba ta zartas da “yarjejeniyar kare ikon yara” ba. A watan Afrilun shekarar 2023, majalisar dattawan kasar Amurka ta ki amincewa da daftarin daidaita dokar tabbatar da adalcin jinsi. A kowace shekara, mata kimanin dubu 54 suna kasa samun aikin yi sabo da samun ciki. Kana mata sama da miliyan 2 da dubu 200 ba sa samun kulawa yadda ya kamata a yayin da suka samu ciki da haihuwa. 

A daya bangaren, a kalla akwai jihohi guda 21 a kasar Amurka, dake hana mata zub da ciki. Kuma adadin rasuwar mata masu juna biyu, da mata masu nakuda ya ninka sau biyu cikin shekaru 20 da suka gabata. Mata na shan fama da matsalar tashe-tashen hankula cikin kamfanoni, da makarantu, har ma da gidajensu. Ana kuma damuwa game da daman zaman rayuwar yara a kasar Amurka, duba da yadda aka fitar da yara da dama daga shirin tallafin kiwon lafiya. Kuma, hare-hare masu nasaba da bindigogi, su kasance babban dalilin da yake haddasa rasuwar yara a kasar Amurka. Matsalar shan kwaya tana kuma karuwa cikin yara da matasan kasar Amurka. An gano cewa, jihohin kasar 46, ba su gabatar da rahotannin bacewar yara dubu 34.8, wadanda suke zama tare da iyeyen riko ba.

Amurka wata kasa ce dake cin moriyar baki ’yan hijira a cikin tarihi da zahirin al’amuranta, amma tana da matsala mai tsanani ta kebancewa da nuna wariya ga baki. Tun daga mummunar "Dokar kebance Sinawa" da aka fitar a shekarar 1882, zuwa "Haramcin shigar da musulmai" na shekarar 2017 wadda kasashen duniya suka yi Allah wadai da ita, manufar kebancewa, da nuna wariya ga baki ’yan hijira ta kasance cikin tsarin hukumomin Amurka. A zamanin nan, batun baki ’yan hijira ya zama makami na jam’iyyu don samun riba da gudun nauyin siyasa, kuma ’yan siyasa sun yi watsi da hakkin baki da alherinsu, an mayar da manufofin baki ’yan hijira a matsayin wani ra'ayi na jam’iyyu na "idan kun goyi bayansa, zan yi adawa da shi", kuma a karshe ya zama wasan kwaikwayo na siyasa, wanda ake amfani da shi don cin gajiyar masu jefa kuri'a. Rikicin baki ’yan hijira ya fada cikin wani mummunan yanayi da ba za a iya warware shi ba, inda ake kama baki ’yan hijira da yara, da yin jigilarsu, da cin zarafinsu, da sauran miyagun ayyuka. Siyasantar da baki ’yan hijira da munafuncin hakkin dan adam iri na salon Amurka, an nuna su a fili a harkar batun baki ’yan hijira.

Kasar Amurka ta dade tana aiwatar da manufar mulkin danniya, da aiwatar da harkokin siyasa bisa karfin tuwo, da daukar matakan soja, da kuma saka takunkumi ga sauran kasashe bisa ra’ayin kashin kanta. Kasar Amurka ta rika mikawa sauran kasashe makamai kamar boma-bomai, hakan ya tsananta halin rikice-rikice a yankuna daban daban, tare da haddasa mutuwa da raunatar fararen hula masu yawa, da kuma rikicin jin kai mai tsanani. Haka zalika kuma, kasar Amurka ta dauki matakan kasancewa mai hura wutar rikici a kasashen waje, ta haifar da babbar illa ga zaman lafiya a sauran kasashe, da keta hakkin dan Adam na kasashen. Har zuwa yanzu, kasar Amurka ba ta rufe gidan kurkuku na Guantanamo ba.

An bayyana fannoni biyar a cikin rahoton, wato kasa tabbatar da hakkin jama’a da na siyasa, da kawo babbar illa ga kasar ta nuna banbancin launin fata, da tsananta yanayin rashin adalci na tattalin arziki da zamantakewar al’umma, da cin zarafin mata da yara, da jefa bakin haure dake zaune a kasar ba bisa ka'ida ba cikin mawuyacin hali, da kuma tada rikicin jin kai sakamakon manufar Amurka ta mulkin danniya.

Kasar Amurka na fuskantar matsalolin keta hakkin dan Adam masu yawa, hakan ya sa hakkin dan Adam ya zama hakki ga mafi karancin al’ummar kasar, kana yake haifar da barazana ga bunsuwar sha’anin kare hakkin dan Adam na duniya baki daya. (Bello, Amina Xu, Maryma Yang, Safiya Ma, Zainab Zhang)