logo

HAUSA

UNECA ta yi kira ga kasashen Afirka da su samar da dauwamammen ci gaba ta hanyar amfani da albarkatu

2024-05-29 14:20:20 CMG Hausa

Hukumar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta MDD wato UNECA, ta yi kira ga kasashen Afirka, da su gaggauta cimma burikansu na neman bunkasuwa, ta hanyar amfani da albarkatun kasa.

Jiya Talata, a yayin taron kolin kawancen albarkatun kasa na kasashen Afirka, wanda aka yi a birnin Nairobi fadar mulkin kasar Kenya, mataimakin babban magatakardar hukumar Antonio Pedro, ya bayyana cewa, daftarin da aka fitar bisa albarkatun kasa na kasashen Afirka, ya samar da wata hanyar musamman ga kasashen nahiyar, ta yadda za su kai ga cimma burinsu na neman dauwamammen ci gaba karkashin kudurorin  SDGs, da kuma Ajandar Afirka ta nan zuwa shekarar 2063. A sa’i daya kuma, zai ba da gudummawa wajen kare nau’o’in halittu a nahiyar Afirka, da kuma kandagarkin sauyin yanayi.

Ya kuma kara da cewa, ya kamata a yi amfani da albarkatun kasa na nahiyar Afirka, wajen bunkasa nahiyar da yin kwaskwarima, yayin da kuma ake tallafawa al’ummomin kasashen Afirka.

Ya ce a halin yanzu, UNECA na yin hadin gwiwa da abokanta, domin taimakawa kasashen Afirka, wajen yin amfani da damammakin raya kasashensu da yankunan su, da kuma kara fahimtar kalubaloli, da damammakin dake gabansu, ta fuskar amfani da albarkatun kasa. (Maryam)