logo

HAUSA

Wani mahari ya budewa daliban wata makaranta wuta a Kamaru

2024-05-29 14:04:58 CMG Hausa

 

Hukumar tsaron kasar Kamaru ta ce a jiya Talata, wani dalibi da dan sanda sun ji rauni, sakamakon harbe-harben bindiga da ake zargin wani dan fafutuka ya yi, a wata makaranta dake birnin Bamenda, wani muhimmin yankin dake arewa maso yammacin kasar mai amfani da harshen Turanci.

Wani jami’in tsaro a hukumar ya ce maharin ya harbi wasu dalibai dake gudanar da jarrabawa a makaranta. Harbin bindigar ya tarwatsa daliban dake makarantar, kana an garzaya da wasu da suka ji raunuka asibiti, yayin da sojoji suka bazama neman maharin. (Amina Xu)