Firaministan kasar Sin ya taya takwaransa na kasar Croatia murna
2024-05-29 14:10:50 CMG Hausa
Kwanan baya, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya aika da sako ga Andrej Plenkovic, domin taya shi murnar sake hawan kujerar firaministan kasar Croatia.
Li Qiang ya ce, huldar abota ta hadin gwiwa bisa dukkanin fannoni tsakanin Sin da Croatia tana bunkasuwa kamar yadda ake fata, kuma bangarorin biyu sun cimma sakamako da dama, bisa hadin gwiwar dake tsakaninsu, misali babbar gadar Peljesac da aka gina a kasar Croatia, wadda ta kasance muhimmiyar alama, mai nuna kyakkyawan hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.
Li ya ce kasar Sin tana mai da matukar hankali ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Croatia, kuma, tana son raba sabbin damammakin da ta samu da kasar Croatia, a yayin da take neman zamanintar da kasa.
Kaza lika, Sin na fatan bangarorin biyu za su hada kai domin zurfafa zumuncin gargajiya, da fahimtar juna a harkokin siyasa tsakaninsu, da kuma karfafa mu’amala, da hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta yadda za a amfani juna, da cimma moriyar juna, yayin da ake daga matsayin dangantaka tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)