Sin ta yi kira da a gaggauta dakatar da bude wuta domin tsaron mata da matasa
2024-05-29 14:32:11 CMG Hausa
Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong, ya gabatar da jawabi a muhawar ministoci mai taken “Gudunmawar mata da matasa ta fuskar kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali” da kwamitin sulhun MDD ya gudanar a jiya Talata, inda ya bayyana cewa, dole ne kasashen duniya su gaggauta dakatar da bude wuta, don kiyaye tsaron mata da matasa.
Fu Cong ya ce, rashin kwanciyar hankali, da yake-yake na ci gaba da addabar duniya, kuma rikice-rikicen da ake fuskanta na kara tsananta, inda abubuwan da suke illata mata da matasa ke matukar karuwa. A cewarsa, ya kamata kwamitin ya sauke nauyin dake wuyansa, na mai da aikin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya a gaban komai, ya kuma taka rawar gani wajen hanzarta matakan aiwatar da tsagaita bude wuta.
Fu Cong ya ce Sin na fatan mabambantan bangarorin da tashe-tashen hankula suke shafa, za su nace ga alkawuransu na kiyaye dokar jin kai ta kasa da kasa, don dakile kaddamar da hare-hare kan mata da matasa, da kuma daukar matakan a zo a gani, na tabbatar da shigar da tallafin jin kai a wuraren dake fama da rikice-rikice, kana da komawa teburin warware matsaloli a siyasance, ba tare da bata lokaci ba.
Jami’in ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da goyon bayan tabbatar da kuduri mai lamba 1325, da mai lamba 2250, wadanda kwamitin ya zartas da su, don baiwa mata da matasa damar shiga aikin wanzar da zaman lafiya, da ma kawar da bambancin ra’ayi da shingaye.
Baya ga wannan, Sin ta yi kira ga kasashe masu wadata da su cika alkawarinsu na ba da tallafi, da taimako a hukumance, ta yadda za a ciyar da sha’anin mata, da matasa da dai sauransu a kasashe masu tasowa gaba. Kaza lika, Sin na goyon bayan zurfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, da koyi da juna a bangaren aiwatar da dabarun raya sha’anin mata, da matasa don cin moriya tare. (Amina Xu)