logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya bada muhimmin umarni game da kara raya hanyoyin mota masu inganci a yankunan karkara

2024-05-29 21:21:48 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasar, kana shugaban kwamitin koli na sojan kasar Xi Jinping, ya bada muhimmin umarni, game da ayyukan raya hanyoyin mota masu inganci a yankunan karkarar kasar.

A cewar sa, an cimma manyan nasarori wajen shimfida hanyoyin mota masu inganci a yankunan karkara, inda manoma suke kara jin dadin rayuwa cikin kwanciyar hankali da yanayin tsaro.

Xi ya jaddada cewa, “A sabon zamanin da muke ciki, ya dace a kara kokarin aiwatar da sabon zagayen kyautata hanyoyin mota a yankunan karkara, da ci gaba da raya hanyoyin mota masu inganci cikin dogon lokaci, don taimakawa jin dadin rayuwa, da sana’o’i, gami da raya kyawawan kauyuka, da samar da tabbacin hidimomi a fannonin da suka shafi samar da wadata ga manoma a yankunan karkara, da farfado da yankunan karkara daga dukkanin fannoni, da gaggauta zamanantar da ayyukan gona da yankunan karkara, da ciyar da zamanantarwa irin ta kasar Sin gaba. (Murtala Zhang)