logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da shirin samar da kamfanin jiragen sama na Air Nigeria

2024-05-28 09:02:03 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da dakatar da shirin samar da kamfanin jiragen sama na Air Nigeria wadda gwamnatin da ta gabata ta kaddamar.

Ministan lura da harkokin sufurin jiragen sama na kasar Mr. Festus Keyamo ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jiya Litinin 27 ga wata a birnin Abuja a zagaye na biyu na taron bayyana nasarorin gwamnatin shugaba Tinubu na tsawon shekara guda wanda ministoci da shugabannin ma’aikatun gwamnatin tarayya ke gudanarwa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Ministan ya ce, ya zamarwa gwamnati wajibi ta yi watsi da shirin bisa la’akari da cewa, akwai kura-kurai da almundahna sosai a cikinsa.

Ya ce ko kadan babu wata alama dake nuna kishin Najeriya a aikin samar da jiragen, inda ya kara da cewa, kamata ya yi aikin samar da jirage mallakin Najeriya ya kasance a hannun ’yan kasa wanda hakan zai sanya kyakkyawan fata ga ’yan Najeriya amma kuma aka sanya son rai a harkar.

Ya ce ko kadan jiragen da aka kawo da sunan Air Nigeria yaudarar ce kawai.

“Ba Air Nigeria ba ne, jiragen Ethiopia ne aka yi kokarin sanya masu tutar Najeriya, wannan shi ne gaskiya ba jiragen Najeriya ba ne, an dai yi masu fentin Najeriya ne kawai, idan haka ne tun da farko me zai hana a yi wa kamfanonin jiragen saman ’yan kasuwa na gida irin wannan fentin, ba za mu amince wasu daga waje su yi amfani da tambarinmu wajen keta sararin samaniya ba.”

Ministan lura da harkokin sufurin jiragen saman ya ci gaba da cewa, dole ne kamfanin jiragen saman Najeriya ya kasance mallakin ’yan kasa ta yadda kaso sittin na ribar ya rinka kasancewa a cikin gida amma ba wata kasa ba. (Garba Abdullahi Bagwai)