logo

HAUSA

Mozambique: An shirya maido da noman alkama bisa tallafin fasahohin kasar Sin

2024-05-28 10:26:35 CMG Hausa

Rahotanni daga kafofin watsa labaran kasar Mozambique, na cewa yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa, na sake farfado da noman alkama ta lokacin rani, a filayen noma na Lower Limpopo dake yankin Xai-Xai, a lardin Gaza na kudancin kasar ta Mozambique.

Gidan rediyon Mozambique dake yankin, ya ruwaito gwamnan lardin na Gaza madam Margarida Chongo na cewa, za a kaddamar da shuka alkama cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, kuma a matakin farko, za a shuke gonakin alkama da fadinsu ya haura hekta 150.

Gwamna Chongo ta kara da cewa, an cimma nasarar dawo da shuka alkama a yankin noman rani na Lower Limpopo ne, bayan kusan shekaru 50 da dakatar da hakan, bisa hadin gwiwar fasahohin noma na kasar Sin, da taimakon kamfanin Wanbao na kasar Sin wanda ya zuba jari. (Saminu Alhassan)