Sin ta bukaci Amurka ta dakatar da goyon bayan masu yunkurin balle Taiwan daga kasar Sin
2024-05-28 21:28:19 CMG Hausa
Kwanan nan ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya fitar da sanarwa, inda ya bayyana damuwa game da atisayen da sojojin kasar Sin suka gudanar a kewayen yankin Taiwan.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning ta amsa tambayar da aka yi mata game da wannan batu, inda ta ce, batun Taiwan, harka ce ta cikin gidan kasar Sin, kana al’amari ne da ba za’a iya barin sauran kasashe su yi masa shisshigi ba, kuma Amurka ba ta cancanci yin magana a kai ba. Ta ce dalilin da ya sa kasar Sin ta gudanar da atisayen soja a kewayen tsibirin Taiwan, shi ne maida martani mai tsanani dangane da jawabin da jagoran yankin Taiwan ya yi a ranar 20 ga watan Mayu, na rura wutar balle yankin daga cikin kasar Sin, kana gargadi ne da kasar Sin ta yi wa sauran wasu kasashe, wadanda ke mara baya ga ‘yan a-ware gami da tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida. Kaza lika, atisayen sojan da kasar Sin ta gudanar, mataki ne da ya wajaba, wanda kuma ya taimaka ga kiyaye cikakken yankin kasar, kuma ya dace da dokoki da ka’idojin kasa da kasa.
A wani labari na daban kuma, firaministar kasar Bangladesh, Sheikh Hasina ta gabatar da jawabi kwanan nan, inda ta soki Amurka da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan Bangladesh. Ta ce, ba za ta nemi samun iko ta hanyar sayar da wani yanki ko kuma ikon mallakar kasarta ba. Game da wannan batu, Mao Ning ta ce, wasu kasashe ‘yan kalilan suna tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe ta hanyar sarrafa babban zabensu, da lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinsu, al’amarin da ya bankado halayensu na nuna babakere da fin karfi a duniya. (Murtala Zhang)