logo

HAUSA

Abdoulkarim Mamane Barmou: Gani ya kori ji!

2024-05-28 15:25:59 CMG Hausa

Abdoulkarim Mamane Barmou, dan jarida ne daga gidan talabijin da rediyo na Jamhuriyar Nijar wato RTN, wanda ya shigo kasar Sin kwanan nan don halartar bikin matasan Sin da Afirka karo na 8.

A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Abdoulkarim ya bayyana wasu wuraren kasar Sin da ya ziyarta a wannan karo, gami da fahimtarsa kan al’adun gargajiyar kasar da suka burge shi. Ya kuma ce, halayen mutanen kasar Sin, musamman yadda suke son baki da nuna musu karamci, ya burge shi kwarai da gaske, wato ba kamar abun da wasu kafafen yada labarai suka fada ba, cewa wai mutanen Sin suna nuna bambanci ko wariya ga baki. Gani ya kori ji!

A karshe, malam Abdoulkarim ya ce zai ci gaba da aikin fadakar da al’umma, game da ainihin abubuwan da suke faruwa a kasar Sin, don bada gudummawa ga karfafa zumunta, da samun fahimtar juna tsakanin kasar Sin da Jamhuriyar Nijar. (Murtala Zhang)