logo

HAUSA

A shirye Sin take ta zurfafa dangantaka da kasashen Larabawa

2024-05-28 21:12:25 CMG Hausa

A yau Talata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, a shirye Sin take ta dauki taron ministocin Sin da na kasashen Larabawa dake karatowa, a matsayin wata dama ta kara zurfafa dangantakar dake tsakaninta da kasashen.

Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da takwaransa na Sudan, Hussein Awad Ali, a gefen taron ministoci karo na 10 na dandalin tattauna hadin kan Sin da kasashen Larabawa, wanda aka shirya budewa ranar Alhamis mai zuwa, a birnin Beijing.

Wang Yi ya kuma gana da takwaransa na Yemen, Shayea Mohsen Al-Zindani, wanda ya zo Beijing domin halartar taron, inda bangarorin biyu suka tattauna game da yanayin tashin hankali a yankin Tekun Maliya, wanda Wang Yi ya bayyana a matsayin mummunan tasirin rikicin Gaza, yana mai cewa abu mafi muhimmanci shi ne dakatar da rikicin Gaza nan take, domin kaucewa fadawa cikin mawuyacin yanayin jin kai, kuma a shirye Sin take ta taka rawar gani wajen warware matsalar. (Fa’iza Mustapha)