logo

HAUSA

Ministan kiwon lafiya na kasa ya kai ziyarar gani da ido a yankin Maradi

2024-05-28 10:30:11 CMG Hausa

Ministan kiwon lafiya, da al’umma da harkokin jama’a na kasar Nijar, manjo kanal Garba Hakimi ya gudanar da wani rangadin aikin gani da ido daga ranar 21 zuwa ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2024, rangadin da ya kai shi yankin Maradi domin halin kiwon lafiya da na jami’an kiwon lafiya.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da rahoto. 

Ministan ya samu rakiyar gwamnan yankin Maradi, babban dan sanda Issoufou Mamane, darektocin kiwon lafiya na tsakiya, abokan hulda, kungiyoyin fararen hulla masu zaman kansu na gida da na waje da ke aiki a bangaren kiwon lafiya, inda tare da su ministan kiwon lafiya ya ziyarci asibitoci da dama, kamar likitar uwa da danta, likitar mata, dakunan shan magani da babban asibitin Maradi, inda ya tattauna sosai tare da jami’an kiwon lafiya.

A Gidan Roumdji, zangon farko, ministan kiwon lafiya ya karbi likitan CSI da kungiyar UNICEF da bankin musulunci BID suka taimaka wajen ginawa domin amfanawa kimanin mutane 16742 da suka rarrabu zuwa kauyuka 16. Haka kuma ya karbi magunguna tan 9, da kungiyar kiwon lafiya ta duniya OMS ta bada.

Zango na biyu ya kai, babban jami’in kiwon lafiya na kasa a jihar Tessaoua, inda ya ziyarci wasu likitoci na jihar har da likitar da kasar Turkiya ta gina a birnin Tessaoua, wanda ta kasance likita da ke kunshe da masana kwararru a fannin tiyata da cututtuka,

Rangadi na uku ya kai shi, a Madaroumfa idan a likitar firji mata suke aifuwa tare da taimakon ungozumai dalilin matsalar tsaro da kuma a likitar Dan Issa dake cikin karo da kwararar masu jinya har ma daga Najeriya.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.