logo

HAUSA

Xi Jinping ya jajantawa gwamnan-janar Papua New Guinea kan bala’in zaftarewar kasa

2024-05-28 14:05:49 CMG Hausa

 

A ranar Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’aziyya ga gwamna-janar na Papua New Guinea Bob Dadae, don gane da ibtila’in zaftarewar kasa da ta auku a kasar a kwanan baya.

A jiya Litinin, gwamnatin Papua New Guinea ta sanarwa ofishin MDD dake kasar aukuwar bala’in na ranar Juma’ar makon jiya, wanda ya yi sanadiyyar makalewar mutane fiye da dubu 2 a karkashin kasa. (Amina Xu)