Kasar Sin ta mayar da martani game da zargin da ministocin kudin kasashen G7 suka yi mata
2024-05-27 21:36:35 CMG Hausa
Yau Litinin 27 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta maida martani game da zargin da taron ministocin kudin kasashen G7 ya yi wa kasarta cewa, wai tana aiwatar da manufofi da daukar matakan da ba na kasuwa ba. Jami’ar ta ce, akwai wasu kasashen yammacin duniya kalilan da suke nuna bambancin ra’ayi kan wasu daidaikun kasashe ko daidaikun kamfanoni, al’amarin da ya sabawa ka’idojin kasuwa. Ta ce kasashen G7 na yunkurin rura wutar rikici cewa, wai kasar Sin tana wuce gona da iri wajen samar da hajoji, da zummar kawo cikas ga hajoji masu amfani da sabbin makamashi da kasar Sin ta samar, al’amarin da ya saba wa hakikanin gaskiya da manufar tattalin arziki, kana, mataki ne na bada kariya ga harkokin kasuwanci, wanda bai dace da moriyar kowane bangare ba.
Kaza lika, yayin da take amsa tambayar da aka yi mata, dangane da kalaman da jami’an gwamnatin kasar Amurka suka furta cewa, wai akwai yiwuwar jirgin ruwan kasar Sin mai aikin gyare-gyare, ya yi amfani da layukan sadarwa dake karkashin tekun Fasifik wajen gudanar da aikin leken asiri, Mao Ning ta ce, gwamnatin Amurka tana shafa bakin fenti gami da matsa lamba ga kamfanonin sadarwa na kasar Sin da na sauran kasashe, domin kirkiro wani babban tsarin sa ido a duk duniya, wanda ita Amurka kadai za ta jagoranta, ba tare da abokin gogayya, da sa idon sauran kasashe ba. A cewar kakakin, kasar Sin na shawartar gwamnatin Amurka wadda ke yunkurin kiyaye babakere a harkokin sadarwar yanar gizo ta intanet, da ta dakatar da shafawa kamfanonin kasar Sin bakin fenti, da daina daukar matakin ban dariya, wanda ta ce ya yi kama da “barawo na kiran kama barawo”. (Murtala Zhang)