A kalla mutane 40 sun rasu sakamakon harin bam da Isra'ila ta kaddamar kan sansanin masu neman mafaka a Rafah
2024-05-27 10:50:17 CMG Hausa
Wani harin bam da dakarun Isra'ila suka kaddamar kan sansanin masu neman mafaka dake Rafah na kudancin zirin Gaza, ya hallaka a kalla mutane 40 tare da jikkata wasu da dama.
Kamfanin dillancin labarai na falasdinawa WAFA, ya ce sojojin Isra'ila sun harba kusan makaman roka 8, kan wasu tantuna dake wani sabon matsugunin jama'a da yaki ya raba da muhallansu, mai kunshe da dubban mutane a kusa da wata ma'ajiyar kayayyaki ta ofishin MDD mai aikin samar da tallafin jin kai ga 'yan gudun hijirar falasdinawa ko UNRWA.
Wasu majiyoyi sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, harin na Isra’ila na da matukar muni, kasancewar ya fada kan yanki mai dandazon jama'a da suka rasa matsugunan su, kuma makaman da aka harba sun fada kan tantunan roba da langalanga, da wasu ababen hawa na fararen hula.
Majiyoyin sun ce jami'an tsaron al'umma, da motocin kwashe marasa lafiya sun fuskanci manyan matsaloli wajen gudanar da ayyukan ceto, sakamakon matsatsin wurin da lamarin ya auku.
Wasu faya fayen bidiyo da suka kewaya shafukan Facebook, sun nuna hayaki ya turnuke, kuma wuta ta mamaye tantunan da ke da mutane a cikin su, ciki har da yara kanana da mata. (Saminu Alhassan)